Bai kasance yana magana ko kira zuwa ga wani takamammen yare ko wata kabila ba, a'a ya tsaya ne don taimakon 'yan Adam ba tare da la'akari da Kabila, launi, matsayi, yare ko kuma inda suka fito ba. Sakon da yake isarwa cikakken sako ne wanda ya kore duk wani abin da zai kawo cikas ga rayuwar mutane. Cikakken sako ne wanda ba kawai ya canza zamanin da aka saukar da shi ba ne, a'a muna iya ganin haskensa da shiriyar da ke cikinsa hatta a wannan zamani.
Kai, wannan wane irin saKo ne! kuma wane ne ya zo da wannan sako? Shin zai iya magance matsalolin wannan zamani (tare da irin ci gaban kimiyya na wannan zamani)? Shin zai iya biya wa mutum buKatunsa musamman ma mutumin wannan zamani? Shin yana da amsoshi ga bukatun dan'Adam na yau da kullum? Shin zai iya zaburar da masana wajen binciken kimiyya? Ina kuma batun kyawawan dabi'u? Shin shi wannan mai sako (Manzo) yana aikata abin da yake fada ko kuwa kawai yana cikin wadanda suke fadan abin da ya yi mugu dadi ne kawai? To 'na'am' ita ce am sa ga duk wadannan tambayoyi da aka yi a sam a da ma wasu tambayoyin daban; ma'ana wannan sako zai iya magance duk wadannan matsaloli. Ba wai kawai jin dadin rayuwar duniya ba, har ma muna iya samun jin dadin rayuwar lahira idan muka yi riko da gaskiya da wannan sako da kuma tafarkin wanda ya zo da sakon. In da mutum zai yi watsi da son zuciyarsa, to da zai iya gane cewa wannan Sako wanda ake kira Musulunci da kuma Annabi na Karshe mai suna Muhammadu, ba wai kawai amfaninsu ta taKaita ga larabawan karni na sha hudu da suka wuce ba ne, a'a suna iya magance rikitattun matsalolin wannan zamani wanda ake kira da zamanin kimiyya (zamani na ci gaba).
Wannan kalma ta Islam (Musulunci) daga Salam (zaman lafiya) take, wadda a 'Istilahance' take nufin mika wuya; wato mika wuya ga Allah Wanda Ya halicci wannan duniya Ya kuma halicci dan Adam a bisa mafi kyan halitta, kuma Ya azurta shi da karfin tunani. Kai wannan abin mamaki ne domin shi wannan mika wuya yakan tsamar da mutum daga mika wuya ga gumaka, wasu ra'ayoyi da wasu camfe-camfe.
Me za mu iya rubutawa a kan mutumin da ya canza mahangar duniya, sannan kuma ya ceci dan Adam daga bata! Wannan abu a fili yake idan muka yi la'akari da cewa shi din nan Allah ne Ya zabe shi don isar da wannan sako, cikakken mutum ne wanda hatta makiyansa sun gagara gano kure (kome kashinsa) a cikin rayuwarsa.
Yaya za mu yi da mutumin da Alkur'ani ya siffanta shi da 'abin kayi' ga mutane (har ma da wadanda za su zo nan gaba). A fili yake cewa Annabi Muhammadu (s.a.w.a) ya tara siffofi na gari kamar hakuri, jarumtaka, hikima, karimci, basira da dai sauran su, wadanda suka zama abin koyi a gare mu.
Saboda kwadayin ilmantar da mutane gaskiyar Musulunci da kuma wane ne Manzon Allah ya sa mu ke farin cikin kaddamar muku da wannan dan karamin bincike dangane da rayuwar wannan fiyayyen halitta (Muhammadu s.a.w.a). Muna fatan masu karatu za su ji dadin wannan aiki kuma su amfana da shi.
Daga karshe muna rokon Allah da Ya karbi ayyukanmu.
Amincin Allah Ya tabbata a gare ka Ya Manzon Allah, ranar da ka aka haife ka, ranar da ka yi wafati da kuma ranar da za a tashe rayayye kana mai ceton wadanda suka yi riko da tafarkinka. ALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMIN.